Sabbin nade-nade a Jama’atu Nasril Islam daga masarautar Zazzau

0
170

Mataimakin shugaban kungiyar Jama’atu Nasril Islam na kasa kuma Sarkin Zazzau, Mai Martaba Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR ya amince da nadin tsohon magatakarda na Hukumar Kula da Larabci da Harkar Musulunci ta kasa (NBAIS), Farfesa Muhammadu Shafi’u Abdullahi, Wakilin Makarantan Zazzau a matsayin Sabon Shugaban Jihar Kaduna na Jama’atu.

Hakazalika, Sarkin ya amince da dakatar da nada dukkan manyan jami’an Makarantar Fasahar Lafiya da ta Jama’atu Zariya nan take. Ya kuma amince da nadin malam Isyaku Abbas a makarantar.

Haka kuma an nada malm Sa’idu Dogara a matsayin sakatare a Jama’atu Nasril Islam a lardin Zazzau da malam Aliyu Zakari a matsayin rajistara da kuma malam Abdulhamid Sambi a matsayin chief accountant.

Har ila yau, mai martaba Sarkin Zazzau ya amince ba tare da bata lokaci ba kan sauke aikin Jami’an Gudanarwa na Makarantan Koyan Aikin Jinya na Jama’atu Nasril Islam wanda ke Zariya. Ya kuma amince da nada malam Isyaku Abbas a cikin kantoman makarantar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here