‘Yan sanda sun kama mutum 3 bisa zargin fyade a Adamawa

0
150

Rundunar ‘yan sanda ta cafke wasu mutane uku da ake zargi da laifin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 15 fyade a karamar hukumar Mayo Belwa da ke jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar SP Suleiman Nguroje ya fitar a Yola ranar Talata.

Ya bayyana sunayen wadanda ake zargin Uzairu Dan-Fulani mai shekaru 25 da Hassan Nasir mai shekaru 25 da Yahaya Edward mai shekaru 26.

“Wadanda ake zargin sun yi garkuwa da yarinyar ne a ranar 20 ga watan Yuli a lokacin da ta hau keke uku daga Mayo Belwa zuwa Ngurore.

“Kwamishanan ‘yan sanda (CP) a Adamawa, Afolabi Babatola, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan laifin da nufin hukunta wadanda suka aikata laifin,” inji shi.

Nguroje ya yi kira ga jama’a da su kiyaye, su kai rahoto ga ‘yan sanda duk wani abu da ake zargin su da aikatawa, sannan su shiga cikin kokarin rundunar na yaki da duk wani nau’i na cin zarafin mata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here