Tsarin raba tallafin N8,000 bazai kai ga talakawan karkara ba – Uba Sani

0
151

Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani ya soki tsarin raba tallafin N8,000 da Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ga matalauta domin rage musu radadi.

Gwamnan ya bayyana tsarin tura wa wadanda za su ci moriyar tallafin ta asusun ajiyar banki a matsayin yaudara.

A wata hira da Gwamna Sani Uba ya yi da gidan Talabijin na Arise, ya bayyana cewa babu wani tabbataccen kundin bayanai da zai iya kayyade takaimaiman adadin ’yan Najeriyar da suka cancanci cin moriyar tallafin.

Haka kuma, gwamnan ya ce muddin aka tafi a kan wannan tsari, to kuwa kashi 70 zuwa da 75 na mutanen karkara musamman a Arewa maso Yamma sai dai su ji kawai ana yi.

“Mutanen da ba sa amfani da asusun ajiya na banki, saboda haka ta wace hanya za a tura musu kudin tallafin da ake ikirarin za a raba.”

Tuni dai Shugaba Tinubu ya jingine shirin bayar da tallafin wanda za a raba wa iyalai matalauta miliyan 12 domin rage radadin cire tallafin man fetur.

Tun kafin a je ko’ina ne dai ’yan Najeriya suka soma sukar tsarin, lamarin da ya tilasta wa Shugaba Tinubu jingine shi da cewar za a yi nazari domin yi masa garambawul.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here