Cutar Diphtheria ta hallaka yara 3 da kwantar da 7 a Kaduna

0
139

Cutar Diphtheria ta halaka ƙananan yara uku tare da kwantar da bakwai a asibiti, bayan ɓarkewarta a ƙaramar hukumar Maƙarfi da ke jihar Kaduna.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN, ya ambato sakataren lafiya na ƙaramar hukumar Makarfi Malam Aliyu Alassan na tabbatar da haka a lokacin zantawa da shi.

Ya ce an samu ɓullar cutar a garin Tashar Na Kawu da ke mazaɓar Gubuchi a ƙaramar hukumar.

Alassan ya ce mafiya yawan waɗanda cutar ta kama ƙananan yara ne, ya ci gaba da cewa tuni aka ɗauki samfurin jininsu tare da aika shi Abuja babban birnin ƙasar domin yin gwaji don tantance cutar .

“An kai waɗanda ake zargi sun kamu da cutar zuwa asibiti, tare da killace su domin ba su kulawar da ta dace”, in ji shi.

Ma’aikatar lafiyar jihar ta tabbatar da ɓullar cutar a wasu garuruwan Kafancan da ke yankin ƙaramar hukumar Jema’a, bayan bayyanar alamomin cutar a wasu unguwanni a garin na kafancan

Cikin wata sanarwa da ya fitar gwamnan jihar Sanata Uba Sani ya umarci ma’aikatar lafiyar jihar da ta gaggauta tura tawagar likitoci zuwa garin na Kafancan domin gudanar da bincike tare da ɗaukar matakan da suka dace kan ɓullar cutar.

A baya-bayan nan cutar mashaƙo na ci gaba da ɓulla a wasu jihohin ƙasar, tare da rahotonnin rasa rayuka masu yawa a wasu jihohin.

Alamomin cutar sun haɗar da wahalar numfashi, da zazzaɓi mai zafi, da tari, da kasala, da zafin maƙogoro da kuma kumburin wuya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here