Gwamnatin Bauchi ta warware rawanin hakimai 6

0
136

Bayan watanni uku da kammala babban zaben 2023, hukumar kula da kananan hukumomin jihar Bauchi ta ware rawunan wasu Hakimai 6 daga Sarautunsu kan zarginsu da shiga harkokin siyasa dumu-dumu. 

Hakiman da abin ya shafa sun fito ne daga Masarautar Bauchi da Katagum.

Babban sakataren hukumar kula da ayyukan kananan hukumomin jihar Bauchi, Nasiru Ibrahim Dewu, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

“Hukumar kula da kananan hukumomi ta Jihar Bauchi ta amince da ware rawunan wasu sarakuna shida daga masarautun Bauchi da Katagum kan shiga cikin harkokin siyasa da samunsu da laifukan da suka hada da rashin da’a, da sare itatuwa, almubazzaranci da dukiyar al’umma da rashin bin doka da oda wanda hakan ya sabawa dokar ma’aikata.

“Masu rike da Sauratu da abin ya shafa sun hada da Hakimin Dubi, Aminu Muhammed Malami, da Hakimin Azare, Bashir Kabir Umar da kuma Hakimin Tafiya, Umar Omar sai kuma Hakimin Tarmasawa, Umar Bani.

“Wadanda abin ya shafa daga Masarautar Bauchi sun hada da Hakimin Beni, Bello Sulaiman da Hakimin kauyen Badara, Yusuf Aliyu Badara,” cewar sanarwar.

Dewu ya kara da cewa an umurci sarakunan da aka kora da su mika ragamar yankunansu ga sakatarorinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here