Majalisar Dattawa ta nemi a daina gindaya sharadin shekaru wajen daukar aiki

0
152

Majalisar Dattawan Nijeriya ta bukaci hukumomin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu su daina gindaya sharadin shekaru kafin su dauki mutum aiki.

Batun ya bijiro ne ranar Laraba bayan da majalisar ta saurari koken da aka gabatar mata game da hakan.

Sanata Abba Moro ne ya gabatar da koken mai taken ‘Ya kamata a dauki mataki kan sharadin shekaru na daukar ma’aikaci a Nijeriya, “Age Requirement Pre-condition for Employment in Nigeria, Urgent Need for Intervention.”

Mista Moro ya ce kayyade shekarun wadanda ake so a dauka aiki ya saba wa babi na 4 da ke da sashi na 42(2) na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 (wanda aka gyara), wanda ya bai wa kowane dan kasar ‘yanci ba tare da nuna masa wariya ba.

Ya ce tanadin dokar aiki ta Kungiyar ‘Yan Kwadago ta Duniya (ILO) ya ce nuna wariya wajen daukar aiki daidai yake da take hakkin dan Adam wanda ke jawo asarar basirar dan Adam abin da kuma yake kawo cikas ga ingancin aiki.

Ya ce hakan na jawo bambance-bambancen zamantakewa ta fuskar tattalin arziki wanda yake kawo cikas ga hadin kan al’umma da kaunar juna da kuma jawo matsala wajen rage talauci.

Mista Moro, wanda tsohon ministan harkokin cikin gida a Nijeriya, ya ce bai kyautu ba a ce bayan dalibi ya kammala digirinsa na farko, idan bai samu aiki ba, sai ya koma jami’a don yin digiri na biyu da fatan idan ya kammala ya samu aiki.

“Abin bai yi dadi ba a ce dalibi a wannan kasa bayan ya kammala yi wa kasa hidima (NYSC) yana da shekara 30, amma kuma ba zai iya samun aiki ba saboda kawai ya wuce shekara 30, wannan abu take hakkinsa ne na dan Adam,” in ji dan majalisar.

Mista Moro ya ci gaba da cewa “wannan halin da ake ciki ya sanya ba a daukar matasan Nijeriya wadanda suke da kwarewa da ilimi da gogewa saboda kawai sun wuce wasu shekaru da aka kayyade.”

Dan majalisar ya ce wannan ya sa da yawa daga cikinsu “suka je suka rage shekarunsu” don yiwuwar samun aikin gwamnati a Nijeriya da sauran kamfanoni masu zaman kansu.

A karshe majalisar dattawan ta bukaci ma’aikatar kwadago da aikin yi ta kasar da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki da su kawo karshen wariyar wadda take dakile damar miliyoyin masu neman aiki.

Ta kuma bukaci ma’aikatar da fito da tsare-tsare cikin hanzari da za su tabbatar da daidaito wajen cin moriyar damar samun aiki a kowane mataki a kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here