Tsadar man fetur: Kungiyar kwalejojin ilimi ta kasa ta Umurci malamai su koma aiki kwana 2 a mako

0
124

Kungiyar kwalejojin ilimi ta kasa (COEASU) ta umurci ‘ya’yanta a fadin Nijeriya da su yi aiki kwana biyu kacal a mako har sai gwamnatin tarayya ta amince da karin albashi zuwa kashi 200 cikin 100.

Dr. Smart Olugbeko, shugaban COEASU na kasa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Laraba.

Olugbeko ya bayyana cewa, an yanke wannan shawarar ne a yayin taron gaggawa na kungiyar a ranar Talata, duba da irin kalubalen da ‘ya’yan kungiyar ke fuskanta wajen zuwa aiki sakamakon tashin doron zabo da farashin man fetur ya yi.

A cewarsa, cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi watanni biyu da suka gabata, farashin litar man fetur ta karu da kashi 250 cikin 100.

“Hakan ya kara ta’azzara hauhawar farashin kayayyaki da kayan abinci da sauran kayayyakin masarufi tare da talauta al’ummar Nijeriya.”

Olugbeko ya yi ikirarin cewa, yanke wannan hukunci na aiki kwana biyu kacal a kowanne mako ya zama dole ne dubi da yadda rayuwa ta yi tsada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here