Gwamnan Kano ya nada El-Mustapha shugaban hukumar tace fina-finai

0
156

Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya naɗa tauraron Kannywood, Abba El-Mustapha a matsayin Sakataren Gudanarwa na hukumar tace fina-finai ta jihar.

Kakakin Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya sanar da wannan naɗin a ranar Litinin.

Abba El-Mustapha wanda ake yi wa taken “Abba na Abba” saboda kusancinsa da gwamnan ya maye gurbin Alhaji Isma’ila Na’Abba Afakallah.

An dai kafa hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ne domin ɗora fina-finai da littattafan Hausa bisa tafarkin adddini da al’adar al’ummar Kano.

Sai dai hukumar ta yi ƙaurin suna wurin kama ƴan Kannywood musamman masu adawa da gwamnatocin dake mulki a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here