NDLEA ta chafke dalibi yana yunkurin fita da kwaya zuwa Turai

0
157

Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya NDLEA sun kama wani ɗalibi a filin jirgin saman Abuja bisa zargin yunƙurin fita da kwayar da nauyinta ya kai kilogiram 7.2 zuwa Turai inda yake karatu.

Dalibin mai suna Benjamin Nnamani Daberechi ya ɗaure kwayar Methamphetamine din da busashen kifi a cikin wani buhu.

An kama ɗalibin ne a lokacin da ake binciken kayan matafiya a lokacin da yake dab da hawa jirgi.

Yayin da jami’an hukumar ke masa tambayoyi a kafin kama shin, Daberechi ya yi ikirarin cewa shi ɗalibi ne da ke karatu a ƙasar Cyrus, to amma da suka fara bincika kayansa sai suka gano kwayar a cikin wani buhu da ya ɗaure busasshen kifi.

Mai magana da yawun NDLEA Femi Babafemi cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce binciken farko ya nuna cewa ƙwayar Methamphetamine ce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here