Matakai 12 da Tinubu ya dauka dan wadata Nijeriya da abinci

0
147

A yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta ba da wani labari mai ban tsoro ranar Laraba kan yadda rashin abinci a duniya ke ta’azzara matsalar yunwa, ita kuma gwamnatin Nijeriya ta fitar da wasu matakai na wadata kasar da abinci.

A ranar Alhamis da maraice ne Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan samar da abinci a Nijeriya.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, shugaban kasar ya bayar da umarnin mayar da dukkan al’amuran da suka jibinci samar da abinci karkashin kulawar majalisar tsaro ta kasa.

“A yau mun ayyana dokar ta-baci tare da kaddamar da wani babban shiri na wadatar da abinci da saukinsa tare da daukar sahihan matakai don magance hauhawar farashi,” in ji shugaban kasar.

Ya kara da cewa shirye-shiryensa za su magance hauhawar farashin kayan abinci sannan su bunkasa harkar noma da samar da ayyukan yi.

“Babu wanda za a bari a baya a kokarinmu na tabbatar da cewa kowa ya wadata da abinci a Nijeriya,” Shugaba Tinubu ya kara da cewa.

Ga dai jerin matakai 12 da shugaban kasar ya bayyana a matsayin wadanda gwamnati za ta bi don tabbatar da wadatar abinci a Nijeriya.

https://platform.twitter.com/embed/Tweet.html?creatorScreenName=undefined&dnt=false&embedId=twitter-widget-0&features=eyJ0ZndfdGltZWxpbmVfbGlzdCI6eyJidWNrZXQiOltdLCJ2ZXJzaW9uIjpudWxsfSwidGZ3X2ZvbGxvd2VyX2NvdW50X3N1bnNldCI6eyJidWNrZXQiOnRydWUsInZlcnNpb24iOm51bGx9LCJ0ZndfdHdlZXRfZWRpdF9iYWNrZW5kIjp7ImJ1Y2tldCI6Im9uIiwidmVyc2lvbiI6bnVsbH0sInRmd19yZWZzcmNfc2Vzc2lvbiI6eyJidWNrZXQiOiJvbiIsInZlcnNpb24iOm51bGx9LCJ0ZndfZm9zbnJfc29mdF9pbnRlcnZlbnRpb25zX2VuYWJsZWQiOnsiYnVja2V0Ijoib24iLCJ2ZXJzaW9uIjpudWxsfSwidGZ3X21peGVkX21lZGlhXzE1ODk3Ijp7ImJ1Y2tldCI6InRyZWF0bWVudCIsInZlcnNpb24iOm51bGx9LCJ0ZndfZXhwZXJpbWVudHNfY29va2llX2V4cGlyYXRpb24iOnsiYnVja2V0IjoxMjA5NjAwLCJ2ZXJzaW9uIjpudWxsfSwidGZ3X3Nob3dfYmlyZHdhdGNoX3Bpdm90c19lbmFibGVkIjp7ImJ1Y2tldCI6Im9uIiwidmVyc2lvbiI6bnVsbH0sInRmd19kdXBsaWNhdGVfc2NyaWJlc190b19zZXR0aW5ncyI6eyJidWNrZXQiOiJvbiIsInZlcnNpb24iOm51bGx9LCJ0ZndfdXNlX3Byb2ZpbGVfaW1hZ2Vfc2hhcGVfZW5hYmxlZCI6eyJidWNrZXQiOiJvbiIsInZlcnNpb24iOm51bGx9LCJ0ZndfdmlkZW9faGxzX2R5bmFtaWNfbWFuaWZlc3RzXzE1MDgyIjp7ImJ1Y2tldCI6InRydWVfYml0cmF0ZSIsInZlcnNpb24iOm51bGx9LCJ0ZndfbGVnYWN5X3RpbWVsaW5lX3N1bnNldCI6eyJidWNrZXQiOnRydWUsInZlcnNpb24iOm51bGx9LCJ0ZndfdHdlZXRfZWRpdF9mcm9udGVuZCI6eyJidWNrZXQiOiJvbiIsInZlcnNpb24iOm51bGx9fQ%3D%3D&frame=false&hideCard=false&hideThread=false&id=1679568213892366336&lang=en&origin=http%3A%2F%2Fwww.trtafrika.com%2Fha%2Fafrica%2Fabin-da-shugaba-tinubu-ya-gaya-wa-yan-majalisar-dattawa-kan-dimokuradiyya-14023713&sessionId=2ea4ae9fe6249f1d269607ed6b5e0bb8a337cd45&siteScreenName=undefined&theme=light&widgetsVersion=aaf4084522e3a%3A1674595607486&width=550px

1. Bai wa manoma da magidanta taki da tsabar hatsi ba tare da bata lokaci ba

2. Hadin gwiwa tsakanin Ma’aikatar Noma da ta Albarkatun Ruwa don samar da ruwa don noma a kowane lokaci na shekara

3. Kirkirar Hukumar Kula da Kayan Abinci don bin diddigin farashi da kula da muhimman wuraren adana kayayyakin abinci

4. Karfafa matakan tsaro ga manoma da gonaki

5. Babban Bankin Nijeriya CBN zai taka rawa wajen samar da kudade ga fannin noma don inganta shi

6. Farfado da eka 500,000 ta kasa domin noma da kuma kogunan kasar don a ci gaba da noman rani

7. Bunkasa bayar da jari da kudade ga fannin noma 8. Inganta sufuri da wuraren ajiyar kayayyakin abinci

9. Kara yawan kudaden shiga daga harkar fitar da abinci da albarkatun noma wasu kasashen

10. Inganta harkokin kasuwanci ta hanyar aiki da hukumar fasa-kwauri ta Nijeriya

11. Samar da dumbin ayyukan yi a fannin noma

12. Mayar da hankali wajen tabbatar da cewa kowanne dan Nijeriya ya samu abinci a kan farashi mai sauki.

A karshe Shugaba Tinubu ya tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa “babu wanda za a bari a baya a wadannan muhimman shirye-shiryen.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here