Kano: Sheikh Aminu Daurawa ya zama shugaban Hisbah

0
253
Daurawa

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sake nada Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa a matsayin shugaban hukumar Hisbah ta jihar karo na uku.

A baya dai, Sheikh Daurawa ya taba jagorantar hukumar har sau biyu, a zamanin mulkin tsohon Gwamnan Jihar, Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma farkon mulkin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Sai dai a shekara ta 2018, Daurawa ya sanar da ajiye mukamin lokacin da aka samu sabani tsakanin Kwankwaso da Ganduje.

Amma a ranar Litinin, malamin ya wallafa wani bidiyo da ya nuna shi yana karbar takardar sake nada shi shugabancin hukumar a karo na uku, daga Sakataren Gwamnatin Jihar, Dokta Baffa Abdullahi Bichi.

Ana ganin malamin ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar gwamnatin jihar mai ci ta jam’iyyar NNPP.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here