Ina yiwa yan Kamaru jinjina da yadda suka tarbe ni – Mbappe

0
147

Tauraron Faransa Kylian Mbappe da yanzu haka ke ziyara can a Kamaru da ke matsayin mahaifar mahaifinsa, ya ce karramawa ce matuka da ya samu damar sanya kafa a tushensa.

A jawabinsa gaban manema labarai, Mbappe mai shekaru 24 ya ce cike ya ke da farin cikin ganinsa a kasar ta Kamaru ta yadda mutane ke ci gaba da nuna masa tsananin kauna.

Dubun dubatar masoya kwallo ne suka tarbi tauraron wanda ya lashe kofin duniya a 2018, bayan isarsa kasar a jiya juma’a wanda ya zama tamkar biki ga al’ummar kasar da ke alfahari da dan wasan.

Wasu masoyan Mbappe yayin tattaunawarsu da manema labarai sun bayyana irin lokacin da suka shafe wajen dakon ranar da dan wasan zai sanyo kafarsa a Kamaru.

Kylian Mbappe wanda ke matsayin kaftin din tawagar kwallon kafar Faransa kuma kaftin din kungiyarsa PSG, haifaffen kasar ta Faransa ne amma kuma mahaifinsa dan Kamaru, yayin ziyarar ya gana da Firaministan kasar Joseph Ngute baya ga wasu jiga-jigan shugabanni.

Wannan ce ziyara ta farko da Mbappe ke kai wa tushen nasa ya na matsayin matashi inda ya gana da manya-manyan ‘yan wasan kasar ciki har da fitaccen dan dambe Francis Ngannou kana Joakim Noah baya ga doka wasa a cikin wata tawagar ‘yan wasa ta Vent d’Etoudi da ke kasar ta Kamaru.

Rahotanni sun ce yayin ziyarar ta Mbappe dan wasan zai kaddamar da wasu ayyukan jinkai karkashin gidauniyarsa wadda ke taimakawa matasa don cimma manufofinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here