Luis Enrique ya zama sabon kocin PSG

0
166

PSG ta nada tsohon kocin Spain da Barcelona Luis Enrique a matsayin sabon mai horas da ‘yan wasanta.

Kocin mai shekaru 53 ya maye gurbin Christophe Galtier wanda kungiyar ta  kora duk da cewa, ya lashe mata kofin gasar Lig 1 a cikin kaka daya tilo da ya jagoranci kungiyar.

Enrique ya kulla yarjejeniyar shekaru biyu da PSG.

A karon farko kenan da Enrique ke aikin horaswa tun bayan da ya  raba gari da tawagar Spain  a cikin watan Disamban bara bayan kasar ta sha kashi a hannun Morocco a bugun fanariti a gasar cin kofin duniya, matakin ‘yan 16.

Ya dai taka rawa a lokacin da yake horas da Barcelona, inda ya lashe mata kofuna tara a kakar wasanni uku tsakanin shekarar 2014 zuwa 2017 da suka hada da kofin gasar zakarun Turai da La Liga da Copa del Rey.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here