Masarautar Zazzau ta dakatar da Marafan yamma kan daukar doka a hannunsa

0
187

Majalisar masarautar Zazzau ta amince da dakatar da Marafan yamman Zazzau bayan wani zama da ta yi.

A wata sanarwa da ta samu sa hannun mai magana da yawun masarautar, Abdullahi Aliyu Kwarbai, ta ce matakin ya biyo bayan samun basaraken da laifin daukar doka a hannunsa.

Sanarwa ta kara da cewa: “A sakamakon haka, Majalisar Masarautar Zazzau ta amince cikin gaggawa da dakatar da Alhaji Mustapha Adamu Ubaidu, Marafan Zazzau daga masarautar har sai abin da hali ya yi.”

Dakatarwar, kamar yadda sanarwar ta nuna ta biyo bayan koken da al’ummar Unguwar Magajiya da ke cikin birnin suka kai wa majalisar.

Masarautar ta ce a shirye ta ke ta dauki tsauraran matakai kan masu rike da mukamai wadanda ke saba wa doka, inda ta bukace su da su mika duk wani batu da ya shafi hukunci ga mahukunta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here