MDD za ta yi taron gaggawa kan yawan kona Kur’ani a Turai

0
124

Kwamitin Kare Hakkokin Dan adam na Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da wani taron gaggawa a cikin kwanaki masu zuwa don magance tashe-tashen hankulan da suka faru a baya-bayan nan kan batun kona Kur’ani a nahiyar Turai, kamar yadda kakakin majalisar ya bayyana a ranar Talata.

“Kwamitin zai gudanar da wata muhimmiyar muhawara ta gaggawa don tattaunawa kan yadda ake samun karuwar ayyukan nuna kyama da kiyayyar addini a bainar jama’a.

“Za mu yi hakan ne duba da yadda ake wulakanta litattafin Kur’ani mai tsarki a wasu kasashen turai da wasu kasashen duniya,” kamar yadda Kakakin Majalisar Pascal Sim ya shaida wa manema labarai.

Pascal Sim ya ba da misali kan bukatar Pakistan a madadin sauran mambobin kungiyar hadin kan kasashen Musulmai a taron.

“Mai yiwuwa a gudanar da muhawarar a cikin wannan makon a lokaci da kuma yanayin da ofishin hukumar kare hakkin dan adam ya tantance a taronsa na yau,” in ji shi.

Lamarin da ya faru a Sweden

Wannan yunkuri dai na zuwa ne bayan kona Kur’ani mai tsarki da aka yi kasar Sweden a ranar Larabar da ta gabata, lamarin da ya janyo cece-ku-ce a dangantakar diflomasiyya da kasashen musulmi.

Salwan Momika, mai shekaru 37, ya ‘tattaka’ Kur’ani mai tsarki tare da kona wasu shafukan cikinsa, a daidai lokacin da Musulman duniya ke shirin gudanar da bukukuwan idin babbar sallah, kuma a daidai lokacin da ake shirin kammala Aikin Hajjin a Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya ce kwamitin kare hakkin Dan adam na MDD mai hedikwatarsa a birnin Geneva, da ke gudanar da wani zama har ranar 14 ga watan Yuli, zai sauya ajandarsa domin gudanar da muhawarar gaggawa kan wannan batu.

Kwamitin hukumar na da mambobi 47. A halin yanzu dai babban kwamitin hukumar kare hakkin dan adam na MDD na gudanar da taronsa na biyu cikin tarukan uku da ya saba yi a kowace shekara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here