‘Yan fashi sun yi sata a fadar Sarkin Minna da rana tsaka

0
208

‘Yan fashi sun kutsa cikin fadar Mai Martaba Sarkin Minna da ke jihar Niger a Najeriya, Alhaji Umar Farouk Bahago da tsakar ranar Talatar nan, inda har suka harbe dogaran da ke tsaron fadar.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, ‘yan fashin sun biyo sahun wani ma’aikacin fadar ne da aka aike shi karbo kabo kudi daga banki.

Rohotan da Daily Trust ta rawaito na cewa, Mai Martaba Sarkin Minna na cikin fadar a lokacin da barayin suka ka yi ta harbe-harben bindiga domin razana jama’a, kuma daga bisani sun yi awon gaba da kudaden da ba a bayyana adadinsu ba.

An dai ce kudaden mallakin Masarautar ce ta Minna, yayin da aka garzaya da dogaran da aka harba babban asibiti don yi musu magani.

Wani mutun da lamarin ya faru a gaban idonsa da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce, ‘yan fashin da makami sun fi karfin ‘yan bangar da aka girke suna tsaron fadar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here