An cafke tsohon kwamishinan Ganduje kan zargin badakalar biliyan 1

0
140

Hukumar Yaki da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC), ta cafke tsohon kwamishinan ayyuka na jihar, kuma tsohon shugaban hukumar gyaran tituna Injiya Idris Wada Saleh.

Rahotonni sun ce hukumar ta cafke tsohon kwamishinan ne bisa zargin badakalar kudi har biliyan daya da sunan gyaran titunan Kano.

Tun da fari an bai wa wasu kamfanoni guda uku North Stone Construction Company Nigeria Limited da Arfat Multiresources Limited da kuma 1st Step Construction Limited aikin.

Hukumar dai na binciken yadda aka fitar da wannan kudi har biliyan daya ba tare da bin ka’ida ba.

Ta kuma zargi cewa, an lissafa wasu tituna da aka ce an yi wa gyara da kudin amma ko kasa ba a zuba ba bare gyara titunan.

Wata majiya a hukumar ta tabbatar wa da gidan rediyon Freedo cewa an sakin kudin a watan Afrilun wannan shekara, bayan da aka ayyana cewar jami’yyar APC mai mulki a lokacin ta sha kasa a zaben da ya gabata.

An gano takardar da aka yi umarnin sakin wannan kudi har biliyan daya ga wadannan kamfanoni uku.

Yanzu haka tuni ma’aikata suka soma bayar da shaida kan yadda aka ba su umarnin gaggauta fitar da wannan kudi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here