Tsadar tumatir: An koma yin miya da yalo a Abuja

0
155

Wasu matan aure a Abuja sun ce sun daina amfani da tumatir a miya saboda farashinsa ya yi tashin gwauron zabi.

Matan sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na ƙasa, NAN cewa sun koma amfani da yalo da karas a madadin tumatir.

Wasu kuma sun ce su na gwada amfani da kabewa ko gwanda da kuma miyar manja wacce aka fi sani da Banga.

Jummai Amodu, mahaifiyar ƴaƴa biyar ta ce ba ta iya mako guda ba tare da yin shinkafa da miya a gidanta ba.

Sai dai ta ce tun da tumatir ya yi tsada yanzu ta koma amfani da yalo wurin haɗa miyar.

Ta ce “Babban bambancin miyar yalo da miyar tumatir shi ne launi.

“Wani lokacin kuma muna amfani da kabewa amma ita ɗanɗanonta na bambanta da miyar tumatir.”

Ga ƙaranci ga tsada

Wata ƴar kasuwa Helen Omo, ta ce ta saba amfani da tumatir amma tsadarsa ta sa dole ta nemi sauyi.

Ta ce “ Jiya na je kasuwa siyan tumatur amma sai na tarar awon da nake saya tsakanin N2,000 zuwa N2,500 ya koma N6,5000.

“Ko taya wa ban tsaya yi ba saboda yafi ƙarfina.”

Mr Chinedu, mai sana’ar hannu ya shaidawa  NAN cewa ƙarancin tumatir ne ya sa yake tsada.

Abin har ya kai wasu masu sayar da kayan miya sun daina sayar da tumatir, kamar yadda Umaru Adamu dake kasuwar Nyanya, Abuja ya shaidawa NAN.

Ya ce tsadar ta sa ko ya saro babu mai saya.

Farashin taki ne ya jawo

Ruƙayya Umar, shugabar kamfanin albarkatun gona na Abraks ta ce hauhawar farashin takin zamani ce ta haddasa ƙarancin tumatir.

A cewarta manoma da dama basu shuka tumatir ba saboda taki yafi ƙarfinsu, shi kuma ba ya kyau sai da taki.

Binciken kamfanin NAN ya nuna cewa kwandon tumatir da a baya ake sayarwa N10,000 ya koma N35,000.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here