An kama ‘yan sandan da suka ‘taka’ wani da mota a Edo

0
138
Edo State Map

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta yi Allah-wadai da abin da ta kira “rashin da’a” da wasu ‘yan sanda suka nuna a Jihar Edo da ke kudancin kasar.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta yi tir da wani bidiyo wanda ya karade shafukan sada zumunta wanda ya nuna wasu ‘yan sanda da suka bi ta kan wani mutum da mota inda rundunar ta ce tuni aka kama su kuma suna a tsare.

“Babban sufeton ‘yan sandan Nijeriya Olukayode Egbetokun ya yi tir da abin da ya faru mai tayar da hankali inda wasu ‘yan sanda suka bi ta kan wani dan kasa da mota a ranar Alhamis 29 ga watan Yunin 2023 a Ekpoma da ke Jihar Edo,” in ji sanarwar.

Haka kuma sanarwar ta ce tuni babban sufeton ‘yan sandan ya bayar da umarni ga ‘yan sandan wadanda ya kira da masu “kunnen kashi” su kai kansu hedikwatar ‘yan sandan da ke Abuja babban birnin kasar domin daukar karin mataki a kansu.

Tun da farko wani bidiyo ya rinka yaduwa a shafukan sada zumunta inda aka ga wani dan sanda a cikin mota kirar Toyota Sienna yana kokarin taka wani mutum kwance sanye da ankwa inda a karshe har ya bi ta kan shi.

Rahotanni sun ce ‘yan sandan sun tsayar da mutumin ne saboda yana tuka mota ba tare da lambar mota ba.

Jama’a da dama a shafukan sada zumunta sun ta Allah-wadai da wannan lamari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here