Mun kama ’yan kwaya 141 a Yobe – NDLEA

0
220

Hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) reshen jihar Yobe ta ce ta cafke mutum 141 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi a Jihar cikin shekara daya.

Hukumar ta ce wadanda aka kama din sun hada da maza 138 da mata uku, kuma an yi kamen ne daga watan Yulin 2022 zuwa Yuni 2023 a fadin Kananan Hukumomin Jihar 17.

Kwamandan hukumar ta NDLEA na jihar Mista Abdulazeez Ogungboye ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Damaturu babban birnin Jihar, domin tunawa da ranar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta duniya

Ya kuma ce an kama jimillar mutum 27, wadanda aka yanke wa hukunci 75 da ke kan shari’a a matakai daban-daban na gwaji.

Abdulazeez ya kuma ce rundunar za ta ci gaba da ayyukan da take yi na kai samame kan masu aikata laifuka ba tare da yin kasa a gwiwa ba musamman wajen yakar al’amuran da suka shafi safarar miyagun kwayoyi da shaye-shayensu a jihar.

Ogungboye ya kuma ce jami’ansu sun cafke miyagun kwayoyin da suka kai kilogiram 304.5 na tabar wiwi kilogiram 125.5 na abubuwan da ke dagula kwakwalwar masu yawa kamar kwayar Tramadol, maganin tari na Kodin da alluran Diazepam da suka kai kilogiram 427.9482 a fadin jihar a shekarar da ta gabata.

Sai dai ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta kafa cibiyar kula da masu shaye-shayen miyagun kwayoyi don dakile matsalar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here