Matsalolin tsaro sun kusa zama tarihi a Najeriya – Gwamna Buni

0
161

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ce, sakamakon sabbin nadin hafsoshin tsaro da shugaban kasa, Bola Tinubu, ya yi alama ce ta kawo karshen matsalolin tsaro da suka addabi mutane a Najeriya.

Buni, ya ce, da nadin sabon mashawarci kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, akwai kwarin guiwar zai yi amfani da kwarewarsa da gogewarsa wajen yakar matsalolin tsaro a Najeriya.

Gwamnan ya bayyana haka a wata sanarwa da daraktan yada labaransa, Mamman Mohammed, ya fitar.

“Shugabannin hukumomin tsaro su na da cikakkiyar kwarewa kuma da gwarin guiwar ‘Yan Nijeriya za su samu nasarar dakile matsalar tsaro.”

Sanarwar ta ce, a matsayinsu na daya daga cikin jihohin da suka sha fama da matsalar tsaro, gwamnan ya jinjina wa gwamnatin tarayya da jami’an tsaro kan nasarorin da suka cimma a jihohin da suke fuskantar kalubalen tsaro.

Gwamnan ya kara da cewa da yunkurin masu ruwa da tsaki da azamar sabbin hafsoshin tsaron akwai kyakkyawar fatan nan gaba kadan matsalolin rashin tsaro za su zama tarihi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here