An saki Yunusa Yellow bayan shafe shekaru a tsare

0
230

Matashin nan dan asalin jihar Kano, Yunusa Yellow Kura, wanda ake tsare tun 2018 ya kubuta bayan dogon lokacin da aka dauka ana shari’arsa bisa zargin dauko wata budurwa mai suna Ese Oruru da ke zaune a kudancin Nijeriya.

A baya dai an tsare Yellow a gidan hali da ke Jibar Bayelsa kafin a dawo da shi jihar Kano.

An ruwaito cewa kakakin hukumar gidan gyaran hali na jihar Kano, Musbahu Lawan Kofar Nassarawa ya tabbatar da sakin Yellow, bisa kammala wa’adin da kotu ta yanke masa.

Tunda fari an zargi Yellow da auren Ese Oruru ba bisa ka’ida ba har aka tsare shi a jihar Bayelsa.

An gurfanar da Yunusa Yellow a gaban babbar kotun tarayya dake Yenagoa, karkashin jagorancin mai shari’a Jane Inyang, inda ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 26 a gidan yari.

Sai dai lauyoyin Yellow da suka hada da Abdul Mohammed SAN, Yusuf Dankofa, Huwaila Mohammed, Sunusi Musa da kuma Kayode Olaosebikan, sun daukaka kara kan rashin amince wa da hukuncin.

Alkalan Kotun daukaka karar karkashin jagorancin JS Iykegh , sun yi watsi da daukaka karar.

Sai dai sun bayyana cewa hukuncin da aka yanke wa Yellow nya sabawa doka, inda alkalan suka amince cewar Yellow ya aikata laifin, sai dai sun rage shekarun zuwa bakwai.

Hukuncin da suka zartar sunce, zai fara ne daga ranar da aka tsare yellow, a shekarar 2018.

Yanzu haka dai Yellow ya fita daga gidan yari, wanda tun abaya ake ta kiraye-kiraye ga shugabannin Arewacin Nijeriya su shiga cikin maganar.

Yunusa Yellow, ya tsinci kansa ne cikin wannan hali sakamakon kaunar da matashiyar ke nunawa Yellow, har ta baro garin su da kanta, kuma ta Musulunta bisa amincewarta sannan suka yi aure.

Amma daga bisani lamarin ya sauya a can garinsu, inda suka ce safararta ya yi zuwa Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here