Chelsea ta ki yarda da tayin Yuro miliyan 55 da Man Utd ta yi a kan Mount

0
150

Chelsea ta yi fatali da tayin da Manchester United ta yi a kan matashin da wasa Mason Mount mai shekaru 25.

Manchester United a Kokarin da take yi na ganin ta kawo Mount Old Trafford ta taya dan wasan na Ingila a kan kudi Yuro miliyan 50 tare da wasu miliyan 5 na tsarabe-tsarabe.

Sai dai Chelsea ta ce dan wasan wanda aka dauko daga karamar kungiya ta Chelsea darajarsa ta fi haka nesa ba kusa ba. Inda ta nemi duk mai son Mount sai ya saye shi da kudi mai tsoka kafin ta iya barin shi ya bar Stamford Bridge.

Ita kuma Manchester United tana duba yiwuwar barin batun Mason Mount Idan har Chelsea ta ki ta sallama shi a kan farashin da suka saye shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here