Masuncin da ya tsinci gawar yaro a komar kamun kifi

0
169

Yayin da adadin baƙin-haure da ke yunƙurin shiga Turai ke ƙaruwa, haka ma adadin waɗanda ke mutuwa sanadiyyar hakan a Tekun Baharrum.

A gefe guda kuma, yayin da ƙasashen Tarayyar Turai ke ɗaukar matakan yaƙi da su, mutanen da abin ya shafa na ci gaba da kokawa kan wahalar rayuwa da ta sanya suke barin ƙasashensu na asali, abin da ke zama gagarumar matsala a gaɓar ruwan Tunisiya.

Daidai lokacin da rana ke fitowa a saman tekun da ke gabashin Tunisiya, masunci Oussama Dabbebi ya fara jawo komarsa idanunsa sun yi ƙuri a kan abin da yake janyowa daga ruwan saboda ba kifi kawai ake samu ba a kodayaushe.

“Maimakon kifi, wani zubin nakan samu gawarwaki. Karon farko na firgita, amma a hankali na saba. Daga baya ma dai janyo gawa a komata ya zama kamar kamun kifi.”

Masuncin mai shekara 30 sanye da ‘yar riga da gajeren wando, ya ce a kwanan nan ya janyo gawar ‘yan cirani 15 cikin kwana uku.

“Wata rana na kamo gawar jariri. Wane irin laifi jariri ya yi wa wani? Na yi kuka. Da a ce babba ne to da ɗan sauƙi saboda ya rayu, amma dai jariri, ai bai ga komai ba,” a cewarsa.

Mista Dabbebi ya saba kama kifi a tekunan da ke garin Sfax na Tunisiya tun yana shekara 10 da haihuwa.

A wancan lokaci, yana cikin mutane masu yawa da ke sana’ar kama kfiin, amma ya ce yanzu da yawa sun sayar da jiragensu ga masu safarar mutane zuwa Turai kan farashi mai tsoka.

A lokuta da yawa, masu safara sun sha yi min tayin kuɗi mai yawa don na sayar musu da jirgina. Kodayaushe sai na ƙi yarda, saboda idan aka yi amfani da jirgina kuma wani ya nutse a ruwa, ba zan taɓa yafe wa kaina ba.”

Wasu baƙin-haure daga Sudan ta Kudu da ke fatan tsallakawa Turai na tafiya a hankali a gaɓar ruwan. Dukkansu na fatan shiga Birtaniya ne.

Ɗaya daga cikinsu ya ce sun haƙura da tafiyar ne zuwa Italiya a karo na biyu saboda cika da jirgin ya yi da kuma rashin kyawun yanayi.

“Akwai mutane da yawa kuma jirgin ƙarami sosai. Mun yi niyyar tafiya duk da haka amma sai aka yi ta iska bayan mun fara tafiya. Iskar ta yi yawa.”

A cewar dakarun tsaron teku na Tunisiya, an tilasta wa baƙin-haure 13,000 komawa gaɓar ruwa a kusa da Sfax saboda maƙare jirgi da suke yi fiye da kima cikin wata ukun farko na wannan shekarar.

Daga Janairu zuwa watan Afrilun wannan shekarar, mutum 24,000 ne suka bar gaɓar ruwan Tunisiya a jiragen wucin-gadi kuma suka shiga Italiya, a cewar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).

Yanzu ƙasar ta zama zango mafi girma na ‘yan gudun hijirar da ke neman shiga Turai. A baya Libya ce kan gaba, amma yawan tashin hankali da zaluncin da baƙin hauren ke fuskanta daga ƙungiyoyin ‘yan daba ya sa suka koma bi ta Tunisiya.

Duk da haka dai, jirgin da ya kife a makon da ya gabata wanda ya kashe mutum 78 da kuma ɓacewar wasu 500, daga Libya ya taso.

Ana iya gane girman matsalar baƙin-hauren a wata maƙabarta da ke kusa da garin na Sfax.

An haƙa ƙaburbura a gefen maƙabartar, inda ake jiran sake afkuwar haɗarin kifewar jirgi a tekun.

Amma duk da haka ba za su isa ba. Yanzu haka ana yunƙurin sake gina wata maƙabartar.

A farkon shekarar nan, akwai wani lokaci da aka kwaso gawarwakin ‘yan ci-rani 200 daga ruwa cikin sati biyu.

Tun daga 2014, mutum fiye da 27,000 ne suka mutu yayin da suke ƙoƙarin tsallakawa Turai, ta tekun Baharrum.

Wannan mummunan hadari da ke cigaba da karuwa ya haifarwa birnin fadawa cikin tsaka mai wuya.

Daraktan hukumar lafiya na shiyyar, Dakta Hatem Cherif, ya ce ba su da isassun kayan aikin da za su iya dakile yawan mace-macen da ake samu.

“Adadin dakin aje gawarwakin da suke da shi bai wuce girman 35 zuwa 40 ba. Wannan shi ne iyakar abin da zai iya dauka, amma yayin da adadin gawarwakin da ake samu yake kara ta’azzara, ya ma zarta adadin da za mu iya karba.”

A kwanan nan an kawo gawarwakin da suka kai 250 dakin ajiyar. Mafi yawansu an jibge su ne a wasu dakuna da ke kusa da juna kuma an dora wasu gawarwakin kan wasu. Koda yake Dakta Cherif ya ce ana kyautata zaton dukkan gawarwakin za a binne su a kaburbura daban-daban.

Galibin wadanda suka mutun ba a tantance su ba, don haka za a gudanar da gwajin kwayoyin halittunsu kuma za a adana sakamakon.

Manufar gwajin shi ne don taimaka wa ‘yan uwan wadanda suka mutu aka binnne su, inda za a iya bincika kwayoyin halittarsu.

..
Bayanan hoto,Bakin hauren Afrika a Tunisiya sun ce su ne aka fi kai wa harin wariyar launin fata

A wani waje mai nisan tafiyar sa’oi uku a mota da ke arewa maso yammacin birnin Tunis, daruruwan tsirarun ‘yan kabilar kasar Tuniya bakaken fata, galibinsu mata ne da kananan yara, sun taru a wani karamin tanti a wajen ofisoshin hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD.

Dukkan su an kwace musu gidaje da ke birnin kuma an kore su daga aikinsu bayan wasu kalaman nuna wariya da shugaban kasar Kais Saied ya furka a watan Fabrairu.

Ya zarge su da boye haramtattun bakin haure da ke shigowa kasar a matsayin wani babban laifi da ke neman lalata yanayin kasa.

An yi ta cece-ku-ce a duk fadin kasar inda wasu ke zargin shugaban da neman dora laifin sakamakon matsanancin karayar tattalin arzikin da kasar ke fuskanta, wanda ya tilasta wa alummar kasar Tunisiya da dama yin gudun hijira.

Game da batun burma wuka da aka samu na baya bayan nan, kan wani matashi dan asalin kasar Saliyo, wadda har yanzu take murmurewa daga yakin basasar kasar da ya kare a 2002, tun bayan jawabin shugaban kasar game batun wuka, matasa da dama sun sari mutane masu yawa a kasar.

“Wasu yaran Larabawa sun kawo mana hari a nan wajen. Yan sanda sun ce za su ba mu tsaro idan mun zauna a nan. Amma idan mun fita daga nan wajen, ba mu da tabbacin samun tsaro.”

Wannnan yanayin mai cike da damuwa da kuma yadda ake cigaba da kame ‘yan adawa ana daure su da tauye hakkin fararen hula da shugaban kasar ke aikatawa, ba su kasance batutuwa mafiiya muhimmanci da jami’an tarayyar Turai ke bai wa fifiko ba sai batun dakile kwararar ‘yan ci rani.

Kawo yanzu a wannan shekarar, sama da bakin haure 47,000 ne suka isa kasar Italya, adadin da ya ninka sau uku idan an kwatanta da makamancin lokacin a shekarar da ta gabata kuma akwai bukatar yin wani abu kan al’amarin.

A lokacin wata kwarya-kwaryar ziyara da tawagar wakilan kungiyar tarayyar Turai suka kai a farkon wannan wata, shugabar hukumar tarayyar Turai, Ursula Von der Leyen, ta yi alkawarin samar da tallafiin kudi da ya kai kusan dala biliyan daya, kwatankwacin yuro miliyan 850.

Idan an samu amincewa, kusan kashi 10 na kudaden za a kashe su ne wajen yaki da safarar bil’adama.

Mummunan al’amarin da ya faru a tekun Girka a makon jiya ya kara nuna bukatar da ake da ita na yin wani abu kan batun.

Yayin da ake kara samun matukar karuwar bakin haure da kuma yadda mutane ke samun kazamar riba wajen safarar bil’adama, dakile yawaitar kananan kwale-kwale da ke jigilar mutanen ba abu ne mai sauki ba.

Ana samun cincirindon bakin haure daga dukkan sassan Afirka da yankin gabas ta tsakiya, wasu na da kudin da suke iya biyan kwale-kwalen, yayin da wasu ke cikin halin ragaita ba su iya biyan kudin abinci da wajen kwana.

Wasu da dama sun rasa takardunsu na fasfo ko kuma an sace, wasu kuma ba su ma yi fasfo din ba sun bar kasarsu ba bisa ka’ida ba.

Duk da yadda ake ta samun hasarar rayukan mutanen da ke neman tsallakawa Turai, amma duk da hakan ana ta samun karuwar masu neman jefa rayukansu cikin hadari, kamar yadda wani matashi dan kasar Gunea ya bayyana.

“Ba za mu iya komawa kasashenmu ba saboda ba mu da kudi ko fasfo. Ba na tsoro. Ina fama da yunwa, akwai tsananin talauci a kasashenmu kuma iyayena ba su da komai. Bana son ‘yayana su yi rayuwa irin wannan. Ina bukatar tafiya.”

Babban hadarin shi ne wannan buri da mutane ke da shi na neman samun ingantacciyar rayuwa yana daga cikin dalilan da ke kara ta’azzara wannan matsala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here