Obama ya soki munafurcin kafafen watsa labaran Yamma

0
128

Tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya yi tir da abin da ya kira ‘munafurcin kafafen yada labaran kasashen Yamma’ musamman kan yadda suke daukar labarai da suka shafi ‘yan gudun hijira.

Obama ya ba da misali da labarin nutsewar jirgin ruwan wasu ‘yan gudun hijira kusan 700 a tekun da ke kudu maso yammacin Girka, inda mutane 82 suka mutu, yayin da ake fargabar daruruwa daga cikinsu sun nutse.

“Yadda aka mai da hankali kan bacewar jirgin ruwan Titan da ya nutse da mutane biyar a tekun Newfoundland na Canada yayin da yake rangadi zuwa wajen tarkacen jirgin ruwan Titanic fiye da ‘yan gudun hijirar da suka nutse a tekun Girka abin takaici ne,” in ji Obama a yayin ziyarar da ya kai birnin Athens na kasar Girka ranar Alhamis.

“Wannan al’amari ne da ke da ban takaici. Kuma, ka sani, za mu iya yin wani abu a kan hakan,” in ji Obama da yake magana kan kwararar ‘yan gudun hijira zuwa kasashen da suka ci-gaba a duniya.

Bambance-bambance a yanayin daukar labarai

‘Yan jarida da masu fafutuka da sauransu sun yi ta ba da fifiko kan batun ceto mutanen da suka nutse a jirgin ruwan Titan fiye da labarin nutsewar ‘yan gudun hijira a tekun Girka.

Jirgin na dauke da maza da mata da kananan yara 750 daga kasashen Syria da Masar da Falasdinu da Pakistan.

Ba a samu mai rai ko gawarwaki ba tun ranar da hatsarin ya faru.

Manyan kafafen yada labarai kamar BBC da CNN da New York Times da wasu kafafen watsa labarai na intanet sun yi ta mayar da hankali wajen rubuce-rubuce da ba da rahotanni kai-tsaye kan aikin ceton jirgin Titan.

Yawancin masu amfani da shafukan sada zumunta sun ce jirgin ruwan ‘yan gudun hijirar ya kife ne a Bahar Rum kuma kuma kasar Girka ta yi jinkiri wajen aikin ceto su, sannan manyan kafafen yada labarai ba su yada rahotanni a-kai- a-kai ba kan wannan batu.

Da dama daga cikin kafafen sun yi ta sharhi ne kan yadda ya kamata a kai daukin gaggawa don ceto mutanen cikin jirgin Titan, a daidai lokacin da rahotanni suka yi nuni da cewa daruruwan ‘yan gudun hijira na jiran sa’o’i a cikin Bahar Rum da fatan za a kai musu daukin gaggawa kafin jirginsu ya nutse.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here