Najeriya ta amince da karin albashi ga Tinubu, Shettima da sauran mukarraban gwamnati

0
125

Hukumar tattarawa da kuma karkasa kudaden shiga ta Najeriya ta amince da karin kasha 114 kan albashin zababbun shugabanni da suka kunshi shugaban kasa, mataimakinsa, gwamnoni da kuma ‘yan majalisun jihohi da na tarayya baya ga alkalai da kuma masu rike da manyan mukaman gwamnati.

  1. Koma shafin farko
  2. Najeriya

Wallafawa ranar: 21/06/2023 – 17:23

Minti 1

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu. REUTERS – STRINGER

Zubin rubutu:Azima Bashir Aminu

TALLA

Hukumar wadda ta ce ta yi amfani da sadarar doka ta 84 da 124 da ta bayar da damar karin albashin ta bukaci dukkanin majalisun dokokin jihohi 36 su tabbatar da bibiya tare da aiwatar da karin albashin ga Gwamnoni da mataimaka da ‘yan majalisu baya ga mataimaka na musamman da kuma masu bayar da shawarwari na musamman da dukkaninsu wannan kari ya shafa.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa tun a jiya talata shugaban hukumar Muhammadu Shehu da ya samu wakilcin kwamishiniyar Tarayyar Rakiya Tanko-Ayuba yayin gabatar da rahoton kunshin dokar ga Gwamnan jihar Kebbi Dr Nasiru Idris ya ce tun a farkon shekarar nan aka kai ga cimma matsayar.

Karkashin sabuwar dokar karin albashin a cewar Muhammadu Shehu wajibi ne kowacce jiha ta tafiyar da shi bisa tanadin dokar kundin tsarin mulki ta shafi na 32.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here