Shari’ar zaɓen Kano: Kotu za ta fara sauraron shaidu ranar Juma’a

0
218

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kano za ta fara sauraron shaidun maƙaraya ranar Juma’a 23 ga Yuni.

Kotun ta sa ranar ne bayan da lauyoyi suka kammala gabatar da takardun ƙorafi da na kariya.

Jam’iyyar APC ce ta shigar da ƙara a madadin ɗan takararta Nasiru Yusuf Gawuna inda take ƙalubalantar nasarar ɗan takarar jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf.

Lauyan APC, tsohon kwamishinan shari’a na jihar Kano Musa Abdullahi Lawan ya bayyana cewa sun shigar da sunayen shaidu 300 gaban kotu.

“Bayan mun fara gabatar da su ne zamu tantance adadin waɗanda za su bayyana gaban kotu daga cikinsu,” in ji Barista Lawan.

A zamanta na baya dai, kotun ta bai wa jam’iyyar APC ta jihar Kano damar nazarin na’urorin BVAS da hukumar zaɓe, INEC ta yi amfani da su wurin gudanar da zaɓen gwamna na ranar 18 ga Maris, 2023.

Na’urorin BVAS ɗin da APC za ta yi nazarinsu sun haɗa da waɗanda aka yi amfani da su a ƙananan hukumomin  Bebeji, Gezawa, Tudun Wada, Garko, Ungogo, Ajingi, Bunkure, Warawa da Ƙaraye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here