Brazil ta sanya baƙar riga don nuna adawa da wariyar launin fata

0
118

Brazil ta sanya baƙar riga a minti 45 ɗin farko a wasan da ta yi nasara a kan Guinea a Sifaniya domin nuna adawa da wariyar launin fata.

Ƙasar ta yankun Kudancin Amurka taƙi sanya rigarta ruwan ɗorawa da ta aka santa da ita a wasan da ta yi nasara da ci 4-1 wanda aka yi a Barcelona.

Wannan ya biyo bayan nuna wariyar launin fata da aka yi wa Vinicius Jr a lokuta da yawa a Sifaniya lokacin da yake bugawa Madrid wasa.

Vinicius ne ya ci fenaritin a mintinan ƙarshe wanda hakan ya bai wa ƙasarsa nasara.

Nuna wariyar da aka yi wa ɗan wasan ra ƙarshe ita ce a wasan da Real Madrid ta buga da Valencia a watan Mayu, bayan nan ƙungiyar ta shigar da kokenta wajen mahukunta.

A farkon wannan watan ne aka hukunta wasu maza bakwai da aka kama da laifin cin zarafin ɗan wasan ta hanyar nuna wariyar launin fata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here