An gano manyan jakunkuna makare da kudade a gidan Emefiele

0
142

Jami’an Tsaron Farin Kaya ta DSS ta gano manyan jakunkunan Ghana Must Go har guda 18 makare da kudade da wasu takardu a gidan dakataccen gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele kamar yadda Jaridar Nigerian Tribune ta rawaito daga sahihiyar majiya.

 

Jaridar ta ce, DSS ta yi awon gaba da jakunkunan bayan ta dauki tsawon yini guda tana gudanar da bincike a gidan Emefiele da ke birnin Lagos a ranar Juma’ar da ta gabata.

Kwanaki takwas kenan da Emefiele ke ci gaba da kasancewa a hannun jami’an DSS da suka tsare shi kuma bayanai na nuni da cewa, akwai yiwuwar ya shafe tarin kwanaki nan gaba a hannunsu a daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan badakalar da ake zargin sa da ita.

Rahotanni na cewa, jami’an na DSS sun tasa keyar Emefile daga birnin Abuja zuwa Lagos, inda suka gudanar da bincike a gidansa, amma tuni aka koma da shi birnin tarayyar bayan gano manyan jakunkunan kudaden da ya adana.

Rahotanni na cewa, jami’an na DSS sun tasa keyar Emefile daga birnin Abuja zuwa Lagos, inda suka gudanar da bincike a gidansa, amma tuni aka koma da shi birnin tarayyar bayan gano manyan jakunkunan kudaden da ya adana.

Yanzu haka DSS ta baza komarta tana neman wani mataimaki na musamman ga Emefiele ruwa a jallo wanda aka ce shi ke rike da mukullai na dukiya da kadarorin da gwamnan bankin ya mallaka a ciki da wajen Najeriya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here