Dan Indiya ya yi tattaki na tsawon shekara zuwa Makka don sauke farali

0
135

Wani dan kasar Indiya ya nuna bajinta, ta hanyar yin tafiyar kafa ta tsawon sama da kilomita 8,600 daga jiharsa ta Kerala zuwa birnin Makka domin sauke farali.

Mutumin mai suna Shihab Chottur daga yankin Balancherry ta Malappuram a kasar Indiya ya taso daga kasar, inda ya ratsa a kasa ta Pakistan, Iran da Kuwait a kan hanyarsa ta zuwa wurin aikin hajjin bana.

Wannan mikakkiyar tafiyar ta cikin kasashe da yankuna da tsaunika da kuma dazuka ta sa ya kwashe kwanaki dai-dai har 370 yana yi.

Shihab ya baro gida domin zuwa kasar Saudiyya ce a ranar 2 ga watan Yunin 2022, ya kuma tsallaka kan iyakar Saudiyya daga kasar Kuwait a mako na biyu na watan Mayun 2023, inda ya fara isa birnin Madina sannan ya wuce Makka a farkon watan Mayun da ya gabata.

Sannan kuma ya yi tafiyar kilomita 440 tsakanin Madina zuwa Makka cikin kwanaki 9 kafin ya isa garin mai tsarki don far aikin Hajji.

A lokacin da ya shiga kasar Saudiyya, ya fara zuwa Madina, daya daga cikin muhimmin wurin gudanar da aikin hajji, bayan ya shafe kwanaki 21 a Madina, sai ya tafi Makka.

A yanzu haka dai Shihab zai yi aikin Hajjin bana tare da mahaifiyarsa mai suna Zainaba wacce ita ma ta isa kasa mai tsarki daga kasar Indiya.

Shihab ya yi ta bayanin tafiyar tasa ta dandalin sada zumunta na Youtube, inda masu bibiyarsa suka yi ta kalon yadda tafiyar tasa ta kaya.

A lokacin tafiyar tasa ya gamu da kalubale a kan iyakar Wagah da ke tsakanin kasashen Indiya da Pakistan, inda ya yi yunkurin shiga Pakistan, amma hukumomin shige da fice na Pakistan suka dakatar da shi, sakmakon wata takardar korafi da aka shigar na hana shi biza ta wucewa.

Da wata kotu ta amince, amma da aka daukaka kara a kotun koli ta kuma sahale ya wuce sai da ya zauna a bakin boda kafin kotun da ke birnin Lahore ta yi watsi da wancan umurnin, aka kuma ba shi bizar wucewa.

Hakan ta sa sai da ya zauna tsawon watanni a wata makaranta da ke garin Wagah don samun takardar izinin shiga kasar Pakistan domin ci gaba da tafiyarsa.

Daga baya ya daukaka kara a kotun koli a kan matakin kotun da ta yi watsi da bukatarsa, kuma a karshe a cikin watan Fabrairun 2023, Shihab ya samu takardar izinin wucewa kuma ya shiga kasar Pakistan, kuma bayan wata hudu, Shihab Chottur ya isa kasa mai tsarki don yin aikin hajjiK.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here