Mutum miliyan 500 na iya kamuwa da cututtuka sanadiyar rashin motsa jiki a cikin shekara 10 – WHO

0
128

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi kira da cewa mutane 500 na iya kamuwa da cututtukan da suke ba masu saurin yaduwa bane kamar ciwoin zuciya,Kiba, cutar siga,tsakanin shekarar 2020 da 2030.

Rahoton da hukumar ta bayar na rashin motsa jiki a shekarar 2022 da aka wallafa ya nuna mutane miliyan 500 na iya kamuwa da cututtukan da ba saurin yaduwa suke yi ba tsakanin shekarar 2020 da 2030, muddin idan har gwamnatoci na kasashen duniya sun kasa daukar matakan da za su inganta motsa jiki.

Rahoton na duniya da yayi bayani kan al’amarin daya shafi motsa jiki na shekarar 2022 ya yi nazari ne kan yadda gwamnatoci ke amfani da shawarwarin da aka basu na yadda za a kara inganta motsa jiki abin ya shafi kowa ba tare da la’akari da shekarunsu ba.

Bayanin halin da ake ciki kan al’amarin motsa jiki daga kasashe 194 ya nuna cewa ci gaban da ake samu bai taka kara ya karya ba,shi ya dace kasashen su kara maida hankali sosai wajen aiwatar da shawarwarin da aka basu na tsare- tsare da manufofi,musamman wajen kula da lafiyar data shafi zuciya,taimakawa ta hanyar dakile kamuwa da cuta,sai kuma rage matsalolin da ake fusknata da suka shafi kula da lafiyar al’umma.

A taimakawa kasashe su kara maida hankali akan motsa jiki wanda tsarin hukumar lafiya ta duniya ne na al’amarin motsa jiki daga shekara 2018 zuwa 2030 k kuma abinda aka fi sani da (GAPPA) da aka bada shawarwari 20.

Wadannan sun hada da hanyoyin mota masu nagarta wanda hakan zai bada dama ga wadanda zasu rika motsa jiki ta tuka Keke, tafiya a kasa,samar da wasu karin tsare- tsare  da bada damr hanyar motsa jiki kamar kula da yara, makarantu, kananan asibitoci, sai wuraren aiki.

Shugaban sashen motsa jiki na hukumar lafiya ta duniya Fiona Bull mutane na asarar abubuwan da suka kamata wajen taimakawa al’amarin motsa jiki kamar hanyoyi, wuraren shakatawa,hanyoyin da Keke ya dace ya bi,da kuma wadanda za suyi tafiya a kasa,duk da yake dai akwai irin wadannan a wasu kasashe.

Rahoton yayi kira da kasashe su dauki motsa jiki shine babbar mafita wajen inganta lafiya domin maganin kamuwa da cututtukan da basu yaduwa,ya kasance an sa al’amarin motsa jiki a dukkan wasu tsare- tsare,sai kuma samar da abubuwan aiki da horarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here