Sobon rikicin makiya da manoma ya yi sanadin mutuwar mutane 13 a Filato

0
143
Fulani Makiyaya
Fulani Makiyaya

Kimanin mutane 13 ne suka rasa rayukan su a yankin karamar hukumar Barikin Ladi da ke jahar Filato, a ci gaba da kaiwa juna harin ramuwar gayyar da ake yi tsakanin makiyaya da manoma.

Wannan dai na zuwa ne kwana daya bayan da aka yiwa wasu makiyaya biyar kwanton bauna aka kuma kashesu a garin Rawuru da ke karamar hukumar, inda ‘yan sa’oi bayan faruwan hakan, wasu dauke da bindigogi suka yiwa garin dirar mikiya suka kuma kashe mutane 8 nan take.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jahar DSP Alabo Alfred ya tabbatar da faruwar harin na biyu, sai dai ya ce bayada masaniyar kashe makiyayan da aka yi.

Ya ce kawo yanzu basu kammala tattara adadin mutanen da suka mutu ba, da kuma na yawan gidajen da aka kona.

Sai dai shugaban kungiyar Fulani makiyaya reshen jahar Nuru Abdullahi ya tabbatar wa jaridar Daily Trust da ake wallafawa a kasar kashe mutanen su biyar da aka yi a lokacin da suka kai dabbobin su kasuwa don saidawa a yankin Bukuru da ke karamar hukumar Jos ta Kudu, kuma ya ce kwamishinan ‘yan sandan jahar da shugaban hukmar tsaro na DSS na da labarin faruwar lamarin.

Ana yawan samun kai hare-haren ramuwar gayya tsakanin makiyaya da manoma a ‘yan kwanakin nan a jahar, inda bangarorin biyu ke zargin juna da fara kai hari.

Ko a watan Mayun da ya gabata, sai dai mutane samada dari suka mutu a sanadiyar hare-haren ramuwar gayya a yankin karamar hukumar Mango da ke jahar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here