Bani kadai na nemi wa’adi na uku ba – Obasanjo

0
160

Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo yace bashi kadai ya bukaci wa’adi na 3 kamar yadda ake ta yayatawa ba, domin gwamnonin da yayi aiki da su a lokacin suma sun nemi a sauya kundin tsarin mulki domin basu damar zarcewa a karagar mulki.

Obasanjo wanda ya dade yana watsi da zargin da ake masa na neman wa’adi na 3 da majalisar dokoki tayi fatali da shi, ya zargi gwamnonin jihohi a lokacin mulkinsa a matsayin wadanda suka kitsa sauya kundin tsarin mulkin wanda bai samu nasara ba.

Tsohon shugaban yace a wancan lokaci, gwamnonin jihohin na nuna cewar shi suke nemawa damar yin tazarcen, amma kuma gaskiyar maganar ita ce nemawa kan su suke yi domin da zaran majalisa ta amince da bukatar, suma sun samu damar da suke bukata kenan.

Yunkurin sauya kundin tsarin mulkin a shekarar 2006 ya samu koma baya lokacin da majalisar dokokin Najeriya a karkashin shugabanta Ken Nnamani tayi fatali da bukatar.

Nnamani ya shaidawa manema labarai cewar sun dauki matakin ne domin kare dimokiradiyar Najeriya ta hanyar sadaukar da mukamansu na siyasa saboda tabbacin da suke da shi cewar shugaba Obasanjo zai musu bita kulli saboda hana shi damar zarcewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here