Gwamnonin Arewa maso yamma sun gana da Tinubu kan matsalar tsaro

0
140

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, tare da wasu gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma sun gana da shugaban kasa Bola Tinubu kan matsalar tsaro.

Ganawar da shugaban kasar ya yi da gwamnonin bakwai, wanda aka gudanar a fadar shugaban kasa, ya gudana bayan babban taron majalisar tattalin arzikin kasa (NEC) a ranar Alhamis.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar Juma’a, ta ce gwamnonin sun gana da shugaba Tinubu domin tattauna matsalolin tsaro da ke addabar yankin.

A baya dai gwamnonin sun halarci taron kaddamar da NEC wanda mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya jagoranta.

“Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, tare da wasu gwamnonin Arewa maso Yamma sun yi ganawar sirri da shugaba Tinubu.

“Taron na daya daga cikin kokarin da gwamnonin ke yi na neman shugaban kasa ya sa baki wajen magance matsalar ‘yan fashi da garkuwa da mutane a yankin Arewa maso Yamma.

“Gwamnonin sun yi wa shugaban kasa bayanin babbar damuwarsu kan matsalolin tsaro a jihohinsu.

“Kafin ganawa da shugaban kasa, gwamnoni bakwai na Arewa maso Yamma sun halarci taron NEC wanda ya samu halartar gwamnonin jihohi 36,” in ji Idris.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here