Spain ta kai wasan karshe na gasar kofin Turai

0
140

Kasar Sifen ta Kai wasan karshe na gasar kofin Turai bayan ta lallasa kasar Italiya 2-1 a wasan kusa da na karshe da suka buga a ranar Alhamis. 

Sifen ce ta Fara jefa kwallo ta hannun Dan wasa Pino a minti na uku da fara wasan amma Ciro Immobile dake buga wasa a Ssc Lazio ne ya farke wa kasarsa ta Italiya kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron raga a minti na 11.

A mintunan karshe na wasanne Joselu ya jefa kwallo a ragar Italiya wanda hakan yasa Sifen ta samu damar buga wasan karshe na gasar kofin kasashen Turai inda zata hadu da kasar Kurotiya wadda ta fitar da kasar Holland a wasan kusa da na karshe da suka buga a ranar laraba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here