Siyasa ta wuce, mu hada kai don ceton jihar mu, gwamna Lawal ya roki sabbin ‘yan majalisa

0
111

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bukaci sabbin ‘yan majalisar dokokin jihar da su hada kai, su yi aiki tare don ci gaban jihar.

Lawal ya yi wannan roko ne a ranar Talata a lokacin da yake ganawa da sabbin ‘yan majalisar da aka kaddamar a zauren majalisar dokokin jihar Zamfara da ke Gusau, babban birnin jihar.

A ranar Talata ne aka kaddamar da majalisar dokokin jihar Zamfara ta 7, an zabi sabbin shugabannin majalisar kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanada.

An zabi Hon. Bilyaminu Ibrahim Moriki (Mazabar Zurmi ta Arewa) a matsayin kakakin majalisar jihar ta 7.

Gwamna Lawal, ya bukaci ‘yan majalisar da su ci gaba da kulla kyakkyawar alaka da bangaren zartarwa na gwamnati don ci gaban jihar Zamfara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here