Za a bude kasuwar cinikin ‘yan kwallo a Ingila daga ranar Laraba

0
123

Za a bude kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo a Ingila daga ranar Laraba 14 ga watan Yunin 2023 zuwa 1 ga watan Satumbar 2023.

Kungiyar za ta iya sayen dan wasan da bashi da yarjejeniya da wata kungiya, haka kuma za a iya daukar aron dan wasa bisa kan doka da kulla kwantiragi.

Haka kuma kungiya za ta iya daukar aron mai tsaron raga da zarar ba wani babban gola da yake da lafiya a kasa.

Haka kuma za a iya ciniki tsakanin kungiyoyin Premier League da na EFL.

Gasar tamaula ta Ingila

Kasuwar cinikayyar ‘yan kwallo a Ingila za ta fara hada-hada daga ranar Laraba 14 ga watan Yunin 2023 zuwa 1 ga watan Satumbar 2023.

Za a iya kara wa’adi a karshen ranar rufe kasuwar idan an kusa kammala wani cinikin ko daukar aron dan wasa, amma lokaci bai bada ikon cimma matsaya ba.

Gasar tamaula ta Faransa

Tun daga ranar 19 ga watan Yuni kasuwar ‘yan kwallo za ta fara ci a gasar Ligue 1 da sauran wasannin, wadda za ta karkare ranar 1 ga watan Satumbar 2023.

Gasar tamaula ta Sifaniya da Jamus da Italiya

Kasuwar cinikayyar ‘yan kwallo a La Liga da Bundesliga da kuma Serie A za ta fara ci daga ranar 1 ga watan Yuli.

Haka kuma za a karkare hada-hada ranar 1 ga watan Satumbar 2023.

Gasar tamaula ta Amurka

Tuni aka ci kasuwar kwallon kafar Amurka daga 31 ga watan Janairun 2023 zuwa 24 ga watan Afirilun 2023.

Za a sake bude kasuwar daga 5 ga watan Yuli zuwa 2 ga watan Agustan 2023.

Ana fara kakar kwallon kafar Amurka daga 25 ga watan Fabrairu, wadda za ta rufe ranar 21 ga watan Oktoban 2023.

Gasar tamaula ta Brazil da ta Argentina

Tuni aka ci kasuwar cinikayyar ‘yan kwallo a Brazil, ana sa ran za a sake yin hada-hada daga 14 ga watan Yuli zuwa 13 ga watan Agustan 2023.

An rufe kasuwar ranar 2 ga watan Fabrairun 2023, sai dai ba a bayyana ranar da za a sake bude ta ba, amma ana sa ran sake cinikayya a cikin Yunin 2023.

Gasar tamaula ta Australia

Kasuwar cinikin ‘yan kwallo a Australia ta ci daga cikin Oktoba zuwa Mayu.

Za kuma a sake bude kasuwar daga 24 ga watan Yulin 2023 zuwa 15 ga watan Oktoban 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here