Najeriya ta gargadi masu cin ganda saboda wata cuta da aka samu

0
148

Sakamakon barkewar cutar a wasu kasashen dake yankin Afirka ta Yamma, ma’aikatar noma da raya karkara a Najeriya ta baiwa jama’ar kasar shawara, musamman masu cin naman ganda da gasasshen kifi da naman dajin da aka fi sani da suna ‘bush meat’ da su kaucewa cin wadannan saboda barazanar da suke da ita na yada cutar, har zuwa lokacin da za’a shawo kanta. 

Babban sakataren ma’aikatar Dr Ernest Afolabi Umakhihe yace an fara samun barkewar cutar ce a arewacin Ghana dake iyaka da Burkina Faso da kuma Togo, abinda ya jefa yankin Afirka ta Yamma cikin hadari.

Sanarwar tace cutar ta bushiya ko kuma anthrax tayi sanadiyar salwantar rayukan jama’a yanzu haka, saboda yadda take kama dabbobi da kuma mutane, yayin da masana suka ce bata barin dabbobin gida da na daji.

Masanan sun kuma bayyana alamun cutar da suka hada da tari da zazzabi da ciwon jijiyoyi wadanda rashin daukar mataki da wuri kan iya haifar da cutar zazzabin nimoniya da na huhu da kuma wahalar numfashi, abinda ke kaiga mutuwa.

Gwamnatin ta kuma gargadi jama’a da su kaucewa zuwa kusa da dabbobin da ba’a musu rigakafi ba, domin ana iya daukar cutar kai tsaye ta numfashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here