Gwamnatin Kano ta ci gaba da rushe gine-gine ba saurarawa

0
130

Gwamnatin jihar Kano ta rushe gine-ginen da aka yi a jikin filin wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata.

Freedom ta rawaito cewa, gwamnatin ta kuma rushe wasu Shaguna da ke jikin makarantar Sakandire ta Ƙofar Nassarawa ta fuskar titin IBB.

Sannan ta rushe gine-ginen da ke jikin makarantun Sakandire na Duka Wuya da ta Goron Dutse.

Ƙarin bayani zai zo muku a labaranmu na An Tashi Lafiya da ƙarfe 6 na safe idan Allah ya kaimu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here