Tinubu ya dakatar da gwamnan CBN Emefiele

0
130

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin ƙasar – CBN Godwin Emefiele daga muƙaminsa.

Sanarwa daga ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayyar ƙasar ta ce an dakatar da gwamnan CBN ne domin a gudanar da bincike sannan kuma ya sauya fasalin harkokin kuɗi a ƙasar.

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan babban banki, Mr Godwin Emefiele, CFR daga ofis ba tare da bata lokaci ba,” in ji sanarwar.

An umurci gwamnan CBN din ya mika ragamar tafiyar da harkokin ofis din ga mataimakin gwamna mai kula da harkokin gudanarwa wanda zai kasance mukadashin gwamna har sai an kammala bincike da kuma sauye-sauye a bangaren kuɗi.

A watan Yunin 2014 ne aka naɗa Mr Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya.

Matakin da shugaba Tinubu ya dauka na zuwa ne kasa da mako biyu da aka rantsar da shi a matsayin shugaban kasar.

A bara ne gwamnan CBN ya fito da sabobbin takardun naira a wani mataki na rage yawan kuɗin da ake amfani da shi.

Tun a lokacin yakin neman zabe, Bola Tinubu ya nuna cewa gwamnatin tsohon shugaba Buhari ta yi kuskure kan sauya takardun kuɗi na naira.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here