Gwamnatin Buhari ta lalata Dala biliyan 19 da sunan gyara matatu – Gwamna Sule

0
115

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa da ke Najeriya, ya ce gwamnatin tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari ta kashe fiye da Dala biliyan 19, a kokarin gyara tsoffin matatun manta, kwatankwacin kudin da aka yi amfani da su wajen gina matatar man Dangote.

Cikin shekaru takwas da ya dauka yana mulkin kasar, gwamnatin tsohon shugaban ta bayar da aikin gyara matatun mai da ke Kaduna, fatakwal da kuma Warii, amma har yanzu babu wanda yake aiki a cikin su.

Bugu da kari, da Dala biliyan 19, Dangote ya samar da matatar mai mafi girma a Afirka, kuma matata ta biyu mafi girma a duniya da wani mutum guda ya mallaka.

Da yake jawabi a wata hira da aka yi da shi a gidan talibijin na Channels, gwamnan ya ce samar da irin wannan babbar mata, shakka babu za ta samar da ci gaba sosai da kuma sauyi a nahiyar Afirka.

Gwamnan ya yi Magana game da batun cire tallafin man fetur, y ace hakan yana da nasaba da rashin matatun mai.

Gwamna Sule ya kuma koka da irin sarkakiyar da ke tattare da kula da matatun saboda bangarori daban-daban da suke da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here