Birtaniya za ta tsugunar da ‘yan ci-rani a cikin manyan jiragen ruwa

0
120

Mista Sunak ya lashi takobin dakatar da ‘yan ci-rani masu tsallakowa ta mashigin ruwan kasar daga arewacin nahiyar Turai a cikin kananan kwale-kawale sakamakon yadda aka samu tarin alkaluma masu yawa na mutanen da suka cikin Birtaniya ta irin wannan hanyar a bara.

Sai dai yanzu, akwai dimbin takardun ‘yan ci-ranin a  gaban gwamnatin kasar da take kokarin tantance su gabanin samar musu da wuraren zaman.

Ana sa ran tsugunar da akalla ‘yan ci-rani dubu guda a cikin sabbin manyan jiragen ruwam da aka yi odar su a baya-bayan nan kamar yadda Firaministan ya fadi.

A wata ziyara da ya kai gabar mashigin ruwan Dover, Firaminista Sunak ya ce, sun tanadi sabbin matsugunai a tsohon sansanin sojin ruwan kasar domin tsugunar da daruruwan mutanen da ke neman mafaka a kasar.

Firaministan ya kara da cewa, za a tsugunar da kimanin mutane dubu 3 a tsohon sansanin nan da karshen shekara, yana mai cewa, wannan matakin zai sassauta wa gwamnatin matsin lambar da take sha wajen biya wa ‘yan ci-ranin makuden kudin otel-otel.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here