NLC ta kaurace wa ganawa da gwamnati kan makomar tallafin mai

0
156
NLC
NLC

Tattaunawar da ‘yan Najeriya suka shafe sa’o’i suna dakon sakamakonta tsakanin kungiyar kwadagon Najeriya NLC da bangaren gwammnati ba ta  gudana ba, kamar yadda aka sa rai.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai aka sa ran za a sake shiga ganawa a karo na biyu tsakanin bangarorin biyu, dangane da batun cire tallafin man fetur, bayan gaza cimma matsayar da aka yi a zangon farko.

Comrade Nasir Kabir sakatarenn tsare-tsare na kungiyar kwadagon ta NLC ya shaida wa sashin Hausa na RFI cewa, ko shakkah babu sun amsa gayyatar da gwamnatin Najeriya ta yi musu a ranar Lahadi, amma fa ba su gana ba, kasancewar ba a cika sharadin da suka gindaya na fara mayar da tsohon farashin litar mai na naira 184 ba.

A halin yanzu dai farashin litar man fetur a Najeriya ya koma daga Naira 488 zuwa 557, kamar yadda kamfanin man kasar na NNPC ya sanar a makon da ya gabata, yayin da ake dakon matakin da ‘yan kasuwar man masu zaman kansu za su dauka kan sabon farashin.

A ranar Talata ake sa ran cigaba da ganawar tsakanin TUC da kuma bangaren gwamnati akan batun cire tallafin man.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here