Rushe Daula: Kamfanin da ya kulla huldar kasuwanci ya garzaya kotu, kan gwamnatin Kano ta biya shi diyyar Naira biliyan 10

0
121

Wani kamfani mai zaman kansa, Lamash Property Limited, wanda ya kulla huldar kasuwanci da gwamnatin jihar Kano kan sake gina otel din Daula, ya bukaci a biya shi diyyar Naira biliyan 10 biyo bayan rushe wurin da Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yi a ranar Asabar.

Kazalika, wani kamfani mai suna White Nig. Ltd wanda shi ma suka kulla yarjejeniya kan tsarin PPP tare da gwamnatin jihar Kano don bunkasa sansanin Hajjin bana a jihar, ya ce abin ya ba shi mamaki da abin da ya kira matakin farko na sabuwar gwamnatin jihar.

Manajin Darakta na kamfanin, Hassan Yusuf Baba, ya ce: “Abin takaicin shi ne mu
ba a sanar da mu ba, mun tashi ne kawai muka ga a kafafen sada zumunta cewa an ruguje dukkan gine-gine. Wannan zalunci ne babba wanda ba za mu nade hannunmu mu ga abin ya faru a jiharmu ba, mun kammala duk wani shiri na garzaya wa kotu domin neman hakkinmu.

Wani mai suna Dan Asabe Abubakar, wanda aka rusa gininsa gabanin ruguje Otal din Daula da kuma Hajj Camp, wanda ya gina rukunin shaguna na Filin Sukuwar Dawaki da ke dauke da dakin motsa jiki, dakin gwaje-gwaje na likitoci, da sauran muhimman sassa, ya koka. yadda ya kashe sama da Naira biliyan 1.4 kan aikin.

Ya fusata kan yadda gwamnatin jihar ke rusa kadarorin jama’a ba tare da bin dokar amfani da filaye ba.

Lamash Property Limited, a cikin wata sanarwa mai suna, ‘GOVERNMENT DEMOLITION OF DAULA HOTEL: OUR STAND’, wacce hukumar gudanarwar ta sa hannun a ranar Lahadi, ta ce za ta shigar da kara Kotu suna masu neman diyyar Naira biliyan 10, wanda shi ne kudin da aka riga aka kashe a aikin.

Kamfanin wanda ya bayyana mamakin yadda sabuwar gwamnatin Kano za ta iya kaiwa ga ruguza wani otel na biliyoyin nairori mallakin ta da ko wace fuska, ta ce an fara aikin ne a karkashin gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje, kan tsarin yarjejeniyar PPP. don samar da ayyukan yi ga jama’a da samar da kudaden shiga ga jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here