Benzema ya bar Real Madrid bayan shekara 14 da ya yi a kungiyar

0
157

Karim Benzema zai bar Real Madrid mai buga gasar La Liga yayin da kwantiraginsa ya kare a wannan watan na Yuni.

A cikin makon nan ne aka bayar da rahoton cewa, an yi wa Benzema tayin kwantaragin shekaru biyu na Yuro miliyan 400 domin ya koma kungiyar Al-Ittihad da ke Saudiyya.

Nan da zuwa wani lokaci ake sa ran Shugaban Real Madrid, Fiorentino Peres zai gabatar da Benzema a gaban taron manema labarai inda shi kuma dan wasan zai yi jawabinsa na bankwana.

Benzema ya shafe shekaru 14 a Bernabeu, inda ya shiga cikin sahun zaratan ’yan wasa mafi zura kwallaye a kulob din kuma ya lashe gasar Zakarun Turai biyar da kofunan La Liga hudu da kuma kyautar Ballon d’Or ta 2022.

An yi tsammanin Benzema mai shekaru 35 zai ci gaba da zama a Madrid na tsawon kaka daya har zuwa watan Yunin 2024, amma ya zabi ya jarraba sa’arsa a wani kalubalen a fagen tamaula.

Duk da raunin da ya yi fama da shi a bana, Benzema ya ci kwallaye 18 a wasanni 23 da ya haska a gasar La Liga, da kuma kwallaye hudu a Gasar Zakarun Turai.

Benzema ya koma Madrid ne daga Lyon a shekarar 2009 kuma zai bar kungiyar bayan ya lashe kofuna 24 ciki har da La Liga hudu, Zakarun Turai biyar, Copa del Rey uku, Spanish Supercopa uku, UEFA Super Cup hudu da kuma Gasar cin Kofin Duniya na kungiyoyi biyar.

Benzema ya ci kwallaye 353 a Real Madrid — fiye da wasu zaratan ’yan wasan kulob irin su Raul Gonzalez da Alfredo di Stefano — sai dai Cristiano Ronaldo ne kadai ya yi masa fintinkau a tarihin kulob wanda ta ci kwallaye 450.

Ya yi ritaya daga buga wa kasarsa ta Faransa ne a watan Disamba yayin da ta sha kashi a hannun Argentina a wasan karshe na Gasar Kofin Duniya na 2022.

Sai dai tun da farko kociyan Faransa, Didier Deschamps ya fitar da shi daga cikin tawagar ’yan wasan bayan ya gaza murmurewa daga raunin da ya samu a lokacin da aka fara gasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here