Boka ya yi tsafi da faston da ya je wajensa neman maganin ‘mu’ujiza’

0
145

Rundunar ’yan sandan jihar Osun ta tsare wani boka mai suna Isiaka Ogunkoya bisa zargin sa da kashe wani fasto, ya yi tsafi da shi bayan faston mai suna Kalejaye Ezekiel ya je wajensa neman maganin da zai ba shi karfin iko da nuna mu’ujiza.

Bayan kama bokan a hanyarsa ta zuwa yankin Isoyin, bokan mai shekara 48 ya yi ikirarin aikata ta’asar tasa.

An kama bokan tare da wasu sassan jikin dan Adam wadanda ya ce na faston ne da ya je wajensa neman maganin da zai rika nuna mu’ujiza.

Bokan ya ce, “Na kashe faston ne na yi tsafi da shi.

“Ina bukatar sassan jikin dan Adam a daidai wannan lokaci sai faston ya zo gare ni.

“Ya shaida min cewa yana son karin mu’ujizoji ta yadda zai dada samun mambobi a cocinsa, sai na ji a raina na samu damar da zan yi amfani da faston in yi tsafin da nake shirin yi a wannan lokaci.

“Na ba shi wani jikon magani ya sha, sai barci ya dauke shi. Sai na yanka shi na fede, na cire zuciyarsa wadda na yi amfani da ita na hada wani magani,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here