Najeriya ce ta 37 a kasashen da suka fi fama da ciwon siga – Kididdiga

0
116

Kasashen Mauritius da Masar su ne suka fi mutanen da cutar siga ta fi kamawa a Afirka, inda suke da kashi 22.60 da kuma kashi 20.90, kamar yadda kiyasin kidid-digar cutar siga ta duniya ya bayyana.

Nijeriya tana da kashi 3.60 na wadanda suka kamu da cutar siga, inda ta kasance kasa ta kuma ta 37 a Nahiyar A fiirka, kafin wasu kasashe 17 da suka hada da Gambia da Benin da suke da kashi 1.90 da 1.10.

Kamar yadda kiyasin bayanan na mutanen da suka kamu da cutar siga na duniya ya nuna mutane masu shekaru tsakanin 20 zuwa 79 a kasashe 211 cikin a 2021, inda aka samu alkalumma daga cibiyar cutar siga ta kasa da kasa (IDF).

Sauran kasashen Afirka da cutar ta fi kamari sun hada da kasar Sudan mai kashi 18.90, Tanzania mai kashi 12.30, Zambia mai kashi 11.90 da Morocco mai kashi 9.10.

Wani kiyasin da aka fitar kashi na 10 ya nuna cewa mutane miliyan 24 masu she-kara tsakanin 20 zuwa 79 suna rayuwa tare da cutar a Nahiyar Afirka a shekarar 2021.
Wannan kiyasin ana ganin zai karu zuwa miliyan 33 nan da shekara ta 2030, inda zai karu da miliyan 55 a shekarar 2045, kamar yadda rahoton ya nuna.

Bugu da kari, akwai wasu miliyan 13 da suke rayuwa da cutar ba tare da an gwada su ba a Nahiyar Afirka, cutar ta yi sanadiyar mutuwar mutane 416,000 a Nahiyar Afirka a shekarar 2021.

Wata kididdigar da ba a dade da fitarwa ba ta nuna a Nijeriya akwai mutane mili-yan shida da suke rayuwa da cutar siga, duk da yake dai ana ganin yawan mutanen da suke rayuwa da cutar yana iya wuce haka, saboda akwai kashi biyu bisa uku na matsalolin da suke da nasaba da cutar siga da ba a yi bincikensu ba.

Kamar yadda kungiyar masu dauke da cutar siga ta Nijeriya ta nuna akwai ‘yan Ni-jeriya fiye da miliyan 8.2 da za su iya kamuwa da cutar siga, yayin da wasu miliyan shida tuni suna rayuwa da ita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here