Tsawa ta kashe yaro dan shekara 5 a Katsina

0
136
Malam Junaidu Gide, mahaifin marigayin mai suna Abdulmalik ya bayyana cewa, “Lokacin da na rufe wurin aiki a tashar mota bayan Sallar Magriba an yi ruwan sama.

“Da ruwan ya lafa na je gida na nemi yara, mahaifiyarsu ta ce min sun tafi masallaci.

“Bayan ’yan mintuna sai ga Abdulmajid yayan marigayin ya dawo gida a firgice, ya ce wani abu mai nauyi ya same su a hanyarsu ta dawowa gida, ga kaninsa yana can kwance a bakin hanya.

“Da muka je wajen, na garzaya da shi Babban Asibitin Funtua inda aka tabbatar da rasuwarsa.”

Gide ya bayyana cewa gawar yaron ta kone daga kirjinsa zuwa kasa, amma “Saboda dare da ruwan sama ruwan sama da ake yi a lokacin, ya sa muka binne Abdulmalik a safiyar ranar Talata kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada.

“An yi tsawa a ranar Litinin da ta gabata daga nan har zuwa Funtuwa, mutane ba su yi mamakin abin da ya faru da dana ba saboda an yi tsawa sosai a ranar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here