Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Kano ya sake sanar da nadin sabbin mukamai

0
131

Gwamnan jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf ya amince da karin nadin mukamai biyar a banagarori daban-daban.

Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya fitar da sanarwar a shafinsa na Facebook a safiyar ranar Alhamis.

Wadanda aka nada sune kamar haka:

  1. Engr. Garba Ahmed Bichi, Manajan Daraktan Hukumar Ruwa ta Jihar Kano
  2. Dr. Rahila Mukhtar, Babbar Sakatariyar Hukumar Kula da Gudunmawar Kiwon Lafiya ta Jihar Kano (KCHMA).
  3. Hassan Baba Danbaffa, Manajan Darakta na Hukumar Kula da Tituna ta Jihar Kano (KARMA).
  4. Arc. Ibrahim Yakubu, Manajan Daraktan Hukumar Tsare-Tsare da Cigaban Birane ta Jihar Kano (KNUPDA).
  5. Abdulkadir Abdussalam, Akanta Janar na Jihar Kano

Nan ba da jimawa ba za a sanar da ranar rantsar da wadanda aka nada domin ba su damar fara aiki nan take.

Sanarwar ta kara da cewa, An daga darajar Laminu Rabi’u daga Sakataren zartarwa zuwa babban darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here