Cire tallafin man fetur ba nan take zai fara aiki ba, sai karshen watan Yuni – Tinubu

0
140

Sabon shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi karin haske game da kalamansa na cire tallafin man fetur a fadin kasar.

A cewar wata sanarwa da masu taimaka masa kan yada labarai suka fitar a ranar Talata, 30 ga Mayu, 2023, “furucin da Shugaba Bola Tinubu ya yi na cewa ‘tallafin man fetur ya kare’ ba wani abu bane sabo da gwamnatinsa ta kirkira.

“Kawai, ya sake nanata halin da ake ciki ne, la’akari da cewa kasafin kudin tallafin man fetur da gwamnatin Buhari ta tsara, ta amince da tallafin ne kawai a rabin farkon shekara.”

Wannan yana nufin cewa, a karshen watan Yunin 2023, Gwamnatin Tarayya za ta kasance bata da wani tanadin kudade don ci gaba da biyan tallafin man fetur.

Shugaban ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya da cewa, kar su shiga wani firgici ko damuwa, cire tallafin ba zai fara aiki nan take ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here